Al'umma

Fulani Ba Su Da Laifi, Martani Ne Suke Mayar Wa Kan Tarwatsa Su Da Aka Yi – Gumi

Shahararren malamin addinin musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa babu wani shugaban Najeriya da ya kashe makiyayan da ba su ji ba gani ba kamar shugaba Buhari.

Gumi ya kasance mai fafutukar tattaunawa da ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin da ke dauke da makamai a arewacin kasar maimakon amfani da karfin tuwo.

Yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard, Gumi ya amsa wasu tambayoyi da suka shafi ‘yan fashi da ta’addanci a yankin Arewacin kasar nan. Ya yi ikirarin cewa kungiyar ta’addanci ta Ansaru, reshe ne na kungiyar Boko Haram da ake tsoro, sun dauki makamai ne a lokacin da aka wargaza sansanonin su da ke dajin.

Advertisement

Ya kara da cewa, Ansaru ba tana kalubalantar Najeriya ne ba, illa dai munanan ayyuka a jihar.

Da aka tambaye shi ko Shugaba Buhari yana da hannu a duk halin da ake ciki a kasa, kamar yadda wasu jama’a ke ikirari, malamin ya ce, “A’a, akasin haka ne. Abin sani kawai kuskure ne. Idan har akwai Shugaban kasa da ya kashe makiyaya da ba su ji ba ba su gani ba a daji, to Buhari ne.

A cikin waɗannan hare-haren bama-bamai, mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, mata, da yara duk suna mutuwa.”

“An fara ne a lokacin gwamnatin Jonathan, ina gaya muku yawancin makiyayan suna maida martani ne kan yadda aka yi amfani da sojoji fiye da kima, ‘ya’yan su sun tarwatse, aka raba su da muhallan su, abin da ya faru ke nan kuma abin da ke faruwa, sai dai fada suke yi.” Na samu damar zama da su na ji koken su.” Ya kuma zargi ‘yan jarida da rashin karbuwa.

Advertisement