Al'umma

Fashewar wata mota a Ghana ta kashe mutane 17, daruruwan gine-gine sun lalace

Wata mota da ke dauke da ababen fashewa da ake amfani da su wajen hakar ma’adanai ta yi karo da wani babur tare da tarwatsa wani gari a yammacin Ghana, inda akalla mutane 17 suka mutu tare da jikkata wasu da dama, a cewar gwamnati.

Hotunan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta a ranar Alhamis sun nuna wani katon wurin da tashin bam ya tashi a yankin Apite da ke kusa da birnin Bogoso mai tazarar kilomita 300 daga yammacin babban birnin kasar, Accra, tare da mayar da gine-gine da dama zuwa tulin itace da bulo da murdadden karfe.

An tabbatar da mutuwar mutane 17 cikin rashin sa’a, sannan an ceto mutane 59 da suka samu raunuka,” in ji Ministan Yada Labarai, Kojo Oppong Nkrumah, a wata sanarwa da ya fitar cikin dare.

Advertisement

Seji Saji Amedonu, mataimakin darakta janar na hukumar kula da bala’o’i ta kasa NADMO, ya ce an lalata gine-gine 500. Wani jami’in agajin gaggawa na yankin ya shaidawa kafafen yada labaran kasar cewa ya ga gawarwaki 10.

Fashewar ta faru ne a lokacin da wani babur ya shiga karkashin wata babbar mota dauke da bama-bamai da ke kan hanyar zuwa ma’adinin zinare na Chirano, karkashin kamfanin Kinross na kasar Canada.

Wani mai magana da yawun kungiyar Kinross ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa lamarin ya faru a nisan kilomita 140 daga mahakar ma’adinan.

Advertisement