Kasuwanci

Fashewar wani abu a wata haramtacciyar matatar mai ya kashe fiye da mutane 100

Sama da mutane 100 ne suka mutu a cikin dare a wata fashewa da aka samu a wani rumbun tace man fetur (Illegal Oil Refining Depot) ba bisa ka’ida ba a jihar Rivers, in ji wani jami’in karamar hukumar da wata kungiyar kare muhalli.

“Fashewar ta barke ne a wani wurin da ake haƙar man fetur Premium Motor Spirit (PMS) ba bisa ka’ida ba kuma ta shafi mutane sama da 100 da suka kone har ba a iya gane su,” in ji kwamishinan albarkatun man fetur na jihar, Goodluck Opiah a ranar Asabar.

Rashin aikin yi da fatara (Unemployment and Poverty) a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur ya sanya tace danyen mai ba bisa ka’ida ba ya zama sana’a mai ban sha’awa amma yana da haɗari.

Ana fitar da danyen mai daga layukan bututun mai mallakar manyan kamfanonin mai kuma ana tace shi zuwa kayayyakin da ke cikin tankunan wucin gadi.

Back to top button