Siyasa

Fara-ministan Libya ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi

Wasu mahara sun kai hari kan motar firaministan kasar Libya Abdulhamid al-Dbeibah da harsashi da sanyin safiyar ranar Alhamis amma ya tsallake rijiya da baya, kamar yadda wata majiya kusa da shi ta bayyana, a daidai lokacin da ake cikin rikici tsakanin bangarorin gwamnati game da jagoranci.

Majiyar ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da Dbeibah ke komawa gida, inda ta bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na kisan gilla, amma maharan sun gudu kuma an mika lamarin domin gudanar da bincike.

Kamfanin dillancin labaran reuters bai ga wani hoto ko faifan lamarin da ya faru ba ko kuma yayi magana da wasu shaidu a kan lamarin.

Advertisement

Idan dai har hakan ta tabbata, yunkurin kashe Dbeibah na iya kara tsananta rikicin kasar Libya bayan da ya ce zai yi watsi da kuri’ar da majalisar dokokin gabashin kasar ta shirya nan gaba a gobe alhamis domin maye gurbinsa.

Advertisement