Al'umma

Fada Ya Kaure Yayin Da Sojoji Ke Kokarin Kwace Wa Yan Sanda Makamai [BIDIYO]

Sojoji da ‘yan sanda sun yi artabu a bainar jama’a kuma an dauki hoton a bidiyo.

Advertisement

Rikicin na zahiri ya faru ne a safiyar yau, 18 ga watan Janairu a ijaya, Apongbo, cikin jihar Legas.

Sojojin sun yi yunkurin kwace makaman jami’an ‘yan sanda inda suka yi artabu.

Advertisement

Wani faifan bidiyo da aka yada ta yanar gizo ya nuna wani soja da dan sanda suna kokawa yayin da abokan aikin su ke musayar kalamai.

Daga karshe ‘yan sandan sun ‘yantar da kan su bayan sun watsa hayaki mai sa hawaye.

“Allah zai hukunta ku” mutane marasa kaki suka fada yayin watsewa.

Ba a dai san abin da ya haifar da arangamar ba.

Kalli bidiyo;

Advertisement