Labarai
Elon Musk Ya Yiwa Mai Kamfanin Facebook, Dariya Bayan Sabis Din Su Ya Dauke
Elon Musk, mai kamfanin Twitter, wanda aka canjawa suna zuwa X, ya yiwa Mark Zuckerberg, mai kamfanin Instagram da Facebook dariya bayan sun samu daukewar sabis, wanda ya tilasta miliyoyin masu amfani da su fita, (logout).
Masu amfani da Facebook da dama sun ba da rahoton matsaloli, ciki har da fita daga Facebook (logout), kuma lokacin da suka yi ƙoƙarin shiga, sun ga saƙon (error), akwai kuskure, “Wani abu ya yi kuskure. Da fatan za a sake gwadawa.”
Akan wannan, Elon Musk ya rubuta a shafin shi na X, cewa “Idan kana ganin wannan sako, to tabbacin sabis din mu yana lafiya lau ne”.