Tsaro

EFCC za ta gurfanar da Okorocha a gaban kuliya bisa zargin damfara na biliyan ₦2.9

A yau Litinin ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, tuhume-tuhume 17 na zamba.

Lamarin ya zo ne sa’o’i kadan bayan Sanatan Imo ta Yamma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Hukumar EFCC ta zargi Okorocha da dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Anyim Nyerere Chinenye da hada baki wajen sace naira biliyan 2.9 mallakin gwamnatin jihar Imo.

Advertisement

Sauran wadanda ake tuhuma da aka jera a cikin karar sune Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited, da Legend World Concepts Limited.

Gwamnatin Imo dai ta sha zargin tsohon gwamnan da wawure dukiyar jihar a tsawon shekaru takwas da yayi yana mulki a jihar.

Gwamnatin ta kuma kwace wasu kadarori da dama da ke da alaka da Okorocha, inda ta ce kudaden ne na almundahana.

Advertisement