Tsaro

EFCC ta gurfanar da dan majalisar tarayya a gaban kuliya bisa zargin zamba ta miliyan ₦185m

A yau Alhamis Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da dan majalisar wakilai, Gabriel Zock a gaban babbar kotun birnin tarayya (FCT) Maitama bisa zargin almundahanar Naira miliyan ₦185.

Advertisement

Hukumar ta gurfanar da Zock wanda ke wakiltar mazabar Kachia/Kagarko ta jihar Kaduna a gaban kuliya bisa tuhumar da ake masa na zamba.

Hukumar EFCC ta yi zargin cewa dan majalisar ya karbi Naira miliyan ₦150 daga hannun wani Adeyemi Kamar don wani fili a gundumar Guzape, Abuja, a shekarar 2015.

Advertisement

Hukumar ta kara da cewa wanda ake kara ya kuma karbi Naira miliyan 35 daga hannun wanda ya kai karar domin saukaka tare da samun takardar mallakar fili.

Laifin, a cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ya ci karo da tanade-tanaden Sashe na 1(1)(a) na babban kudin zamba da sauran laifukan da suka shafi zamba, 2006 da hukuncin da ke karkashin sashe na 1(3) na wannan dokar.

Zock, duk da haka, ya musanta aikata laifin.

Mr. O.S. Adeyemi, wanda ya wakilci lauyan wanda ake kara a kotu, ya mika takardar neman belin dan majalisar.

Mai shari’a Halilu Yusuf ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a hannun EFCC har sai an saurari bukatar belin sa.

Ta dage sauraron karar har zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu

Advertisement