Laifuku

EFCC Ta Cafke Dan Sanda Mai Ritaya Bisa Laifin Buga Jabun Kudi

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta sanar da cewa jami’anta sun kama mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, DSP, Idris Yusuf da wasu mutane biyu mai suna Hassan Abubakar da Ibrahim Yusuf, a jihar Nasarawa bisa laifin yin jabun kudaden.

A wata sanarwa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fitar a ranar Juma’a 20 ga watan Junairu, 2023, an kama wasu mutane uku da ake zargi da yin jabun kudaden ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu, 2023, a unguwar New Nyanya da ke jihar Nasarawa, biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan ayyukansu na tuhuma.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, sun kama wasu da ake zargi da laifin karkatar da kudin jabun da ke da alaka da wani mataimakin Sufeton ‘yan sanda, DSP Idris Yusuf mai ritaya, tare da Hassan Abubakar da Ibrahim Yusuf.

Advertisement

“An kama mutanen uku ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu, 2023 a New Nyanya, jihar Nasarawa, bayan bayanan sirri da aka samu kan ayyukansu na jabu.

“Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.”

Advertisement