Laifuku

EFCC Ta Bayyana Dan Takarar Sanatan Kano Na APC Wanda Ta Ke Ne Ruwa Ajallo

A ranar Litinin Hukumar Yaki da yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da ke Kano ta bayyana dan takarar sanata na jam’iyyar APC, AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda ta ke nema ruwa ajallo bisa zargin zamba.

Lauyan EFCC, Ahmad Rogha ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin a babbar kotun tarayya da ke Kano a cigaba da shari’ar dalar Amurka miliyan $1.3 da ake yiwa Zaura.

“Muna neman Zaura, kuma za a kama shi da zarar mun same shi, kuma a ka’ida ya kamata a ce yana hannun mu kuma kotu ta tabbatar da haka amma ina tabbatar maka za a kama shi a gurfanar da shi a gaban kotu a gaba dage ranar 30 ga Janairu 2023.”

Advertisement

Har ila yau, a kalubalantar shi, lauyan wanda ake tuhuma, Ibrahim Garba Waru ya zargi matakin na hukumar EFCC.

Ibrahim ya dage cewa hukumar ba ta da hurumin kama wanda yake karewa a doka.

Advertisement