Siyasa

ECOWAS za ta gudanar da wani taro na musamman kan juyi mulki a Burkina Faso

Kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka za ta gana a ranar Juma’a domin tattauna rikicin kasar Burkina Faso, inda jami’an soji suka tsige shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore, in ji kungiyar.

Tuni mambobi 15 na kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka da suka hada da Burkina Faso suka yi Allah wadai da juyin mulkin na ranar litinin, wanda ya zo a daidai lokacin da ake kara fusata kan matakin da Kabore ya dauka kan tashin hankalin da kungiyoyin masu dauke da makamai suke yi.

Za a fara taron na musamman kan Burkina Faso da karfe 10:00 agogon GMT a ranar Juma’a, in ji kungiyar ECOWAS a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Advertisement

Wata majiya a jam’iyyar hambararren shugaban kasar ta fada a baya cewa Kabore “yana cikin koshin lafiya” kuma sojojin na tsare da shi a wani gida, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Advertisement