Labarai

ECOWAS: Ƙasashen Burkina Faso, Mali Da Nijar Sun Kafa Wata Sabuwar Ƙungiya

A ranar Lahadi, 7/7/2024 shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS suka fara babban taron su karo na 63 a Abuja ba tare da takwarorin su na kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar ba.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, ya bude taron ne da misalin karfe 1:00 na rana inda ya gode wa takwarorin shi bisa goyon bayan da ya samu daga gare su a shekarar da ta gabata.

Wa’adin Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS ya kare ne a wannan taro na musamman, haka kuma qn sake zabar shi a matsayin shugaban ECOWAS wa’adin da zai fara daga  a ranar 9 ga watan Yuli.

Haka zalika, Tinubu zai jagoranci ECOWAS wajen tattaunawa kan kasashe ukun da suka zabi tafiya ta daban.

A ranar Asabar 6 ga watan Yuli ne mutanen uku suka kaddamar da kungiyar tasu wadda suka sanyawa sunan Sahel Alliance.

Sarakunan sojan Burkina Faso da Mali da Nijar sun kafa wata sabuwar kungiya a hukumance a yayin ganawar da suka yi a birnin Yamai, inda suka yanke hulda da ECOWAS kwana guda kafin ECOWAS ta fara taronta.

Wannan dai na zuwa ne duk da babban abin da taron na ECOWAS ya mayar da hankali a kai shi ne tattauna hanyoyin kwantar da ‘yan tawayen uku bayan da wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka suka yi kira da a koma tattaunawa da su.

Burkina Faso, Mali da Nijar sun sanar da yarjejeniyar kawancen kasashen Sahel da aka fi sani da kawancen kasashen Sahel a watan Satumban da ya gabata na 2023.

Dangane da karfin kawancen, kasashen uku sun kuduri aniyar bada hadin kai idan har aka kai musu hari daga waje.

Kasashen uku sun bar kungiyar ta ECOWAS a watan Janairun wannan shekara ta 2024 bayan ECOWAS ta yi fatali da gwamnatocin soja da suka hambarar da shugabancin dimokuradiyya a wadannan kasashe.

Da yake jawabi yayin taron su a birnin Yamai ranar Asabar, Janar Abdourahamane Tchiani na Nijar ya bayyana kungiyar ECOWAS a matsayin barazana ga kasashen da sojoji ke jagoranta.

Ya ce kasashen uku za su gudanar da kawance ba tare da tasirin kasashen waje ba ga al’ummar su.

Burkina Faso ta yi juyin mulki, wanda ya kifar da dimokiradiyyar farar hula a cikin watan Satumban 2022; Mali a watan Agusta 2021 da Nijar a Yuli 2023.