Tsaro

Ebonyi APC ta zargi PDP da haddasa rikici, rashin jituwa a jihar

Jam’iyyar APC reshen jihar Ebonyi, ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP, tare da gargadin tayar da rikici a jihar ta hanyar kalamai masu tayar da hankali.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ebonyi, Cif Stanley Okoro-Emegha, ya fitar ranar Alhamis a garin Abakaliki.

Hakan ya biyo bayan wani rahoto da aka fitar a wani sashe na kafafen yada labarai, mai taken “PDP na zargin gwamnatin Ebonyi a kan sanarwar da aka ayyana tsohon memba na majalisar wakilai wanda ake nema ruwa ajallo.”

Advertisement

Okoro-Emegha ya shawarci jam’iyyar PDP da ta guji rura wutar yaki da tashe-tashen hankulan siyasa a jihar.

A cewar Shugaban jam’iyyar APC, Gwamna Dave Umahi ya bayyana cewa ana neman tsohon dan majalisa, Mista Linus Okorie kan wannan muguwar yada labaran da aka yi masa.

Ya kuma kara da cewa furucin Okorie na iya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna jihar.

“Ku tuna cewa gwamnonin jihohi sune manyan jami’an tsaro na jihohinsu daban-daban.

A kan haka ya zama wajibi a kansu su samar da hanyoyin da suka dace ta hanyar da ta dace da kuma tabbatar da cewa rantsuwar tabbatar da rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar da suka dauka ba ta cikin hadari.

“Shin kuna tsammanin gwamnan zai nade hannuwansa bai yi komai ba lokacin da tsohon dan majalisar ya yi wani bugu na ruguzawa a facebook wanda ya zama tabarbarewar tsaro?

“Shin kuna sa ran gwamnan zai nade hannunsa ya kalli rikicin da ya dabaibaye jihar?

Advertisement