Al'umma

Dubu Ta Cika: Yadda wani dan tauri ya cakawa cikin shi wuƙa a wajen wasar tauri

Rundunar yan sandan jihar Kano dake Arewacin Nageriya ta hannun kakakin ta DSP abdullahi Haruna kiyawa ta tabbatar faruwar wannan lamarin na bacin rana ga wani shahararren ɗan tauri a Kano.

Kamar yadda bayanai suka nuna, wani ɗan tauri mai suna Nadabo Alhassan ya gamu da bacin rana inda ya daɓawa cikin shi zabgegiyar wuƙa a yayin bikin tauri a kanon ta dabo tumbin giwa kwanakin baya.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru be a garin Gani dake karamar hukumar Sumaila a jihar Kano a wata Lahadi wacce Nadabo ba zai taɓa mantawa ba.

Advertisement

Tun farko dai kafin bikin taurin Alhassan wanda ka bayyana cewa yana da shekaru arbain 40 a duniya, yazo ana tsakiyar wasan taurin yayi kirari – yayi kirari sai kuwa ya fara dabawa kan shi wuƙar a sassan jikin shi.

A dai dai lokacin da Alhassan ya rufe indon shi ya fara gwabzawa kan shi wuƙar ba ƙakkautawa sai abokan shi suka fara cewa ya isa! ya isa!! hakan. Amma kash, tsumin tauri ya tashi ai kuwa kafin kace komai sai ga tumbin Alhassan a waje.

Tuni dai sanarwar tace Alhassan sai ya fadi kasa sumamme cikin jini.

Ba tare da ɓata lokaci ba aka kira yan sanda zuka zo suka garzaya asibiti da shi.

Daga wannan lamarin sai wasar ta tsaya cak, yayin da Alhassan ke kwance a asibiti, kamar yadda yan sanda suka sanar.

Madoga: Gidanlabarai

Advertisement