Tsaro

Dubban mutane a Mali na murnar korar jakadan Faransa daga kasar

Dubban masu zanga-zangar kin jinin Faransa sun yi tururuwa a kan titin Bamako babban birnin kasar Mali, domin nuna murna da korar jakadan Faransa.

Advertisement

Bikin na ranar Juma’a, inda mutane suka daga tutocin kasar Rasha tare da kona kwali da aka yanke na shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya zo ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun takun saka tsakanin kasar da ke yammacin Afirka da tsohuwar mulkin mallaka.

Akwai dubbai da dubbai da dubunnan ƴan ƙasar Mali a yau waɗanda suka ce ‘A’a’ ga Faransa. Don haka abin da Tarayyar Turai da Faransa ya kamata su yi shine mutunta hukumomin Mali,” Moulaye Keita, mamba a majalisar mika mulki ta kasar, ya shaida wa manema labarai.

Advertisement

Keita ya kara da cewa, “Suna bukatar fahimtar cewa hukumomin da ke da iko a yau su ne kadai za su iya yin magana da kasar mu.”

Rikicin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da manyan kasashen yammacin duniya ke cewa an jibge sojojin haya na Rasha da ke aiki da kungiyar Wagner mai cike da cece-kuce a kasar Mali, kasar da ke tsakiyar rikicin da aka dade ana fama da shi a yankin Sahel, inda aka girke dubban sojojin Faransa domin yakar kungiyoyi masu dauke da makamai.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu na kara tabarbarewa ne bayan da sojoji, wadanda suka kwace mulki a watan Agustan 2020, sannan kuma a watan Mayu, suka janye wa’adin gudanar da zabe a watan Fabrairu tare da ba da shawarar ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2025.

Rikicin dai ya yi kamari ne a makon da ya gabata inda aka baiwa jami’in diflomasiyyar na Faransa wa’adin sa’o’i 72 ya fice daga kasar. Kungiyar EU ta ja baya a ranar Juma’a ta sanya takunkumi kan wasu manyan jami’an gwamnatin rikon kwarya na kasar, ciki har da Firayim Minista Choguel Maiga na wucin gadi.

Advertisement