Kasuwanci

DSS Ta Bai Wa Kamfanin NNPC Da Ƴan Kasuwa Awa 48 Su Magance Matsalar Ƙarancin Mai

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta baiwa kamfanin man fetur na kasa (NNPC) Ltd da ‘yan kasuwar mai wa’adin sa’o’i 48 su samar da man fetur ga ‘yan Najeriya.

Layukan man fetur sun sake kunno kai a Legas da sauran sassan kasar inda gidajen mai na sayar da kayayyakin a tsakanin ₦250 zuwa ₦275 kowace lita.

Har ila yau, masu gudanar da kasuwancin baƙar kasuwa suna yin ranar fage suna sayar da man a farashi mai tsada ga masu amfani.

Advertisement

Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar wa manema labarai umarnin bayan wata ganawar sirri da hukumar ta yi da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur a Abuja.

Yace hukumar ta DSS za ta fara gudanar da ayyukanta idan masu ruwa da tsaki suka kasa bin umarnin a karshen wa’adin.

Kakakin ya koka da yadda wannan karanci ya yi wa ‘yan Najeriya tare da yin kira da a gaggauta magance rikicin.

Advertisement