Siyasa

“Dole Sai Anyi Zaɓen Anambra” – Dokubo Asari Ya Ƙalubanci Yan Ƙungiyar Biyafara

Tsohon mai fafutuka a yankin Niger Delta Asari Dokubo, ya bayyana cewa dole ne a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2021 kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta tsara.

Shugaban sashen yada labarai da sadarwa, Uche Okafor-Mefor ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda ya bukaci masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) da kada su hana al’ummar jihar kada kuri’a.

Sanarwar tace dokar zama a gida da masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara suka saka ta kasance laifi, yayin da ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta janye jami’an tsaron da aka tura yankin Kudu Maso Gabas, inda ta yi nuni da cewa a za’a daina amfani da salon tsangwama kan ‘yan kabilar Igbo, domin ba za’a lamunta ba.

“Bisa la’akari da rikice-rikicen dake faruwa, kalubalen tsaro da sauran batutuwa daban-daban da ke damun fararen hula na asali sun haɗu tare ba tare da son ransu ba a Najeriya

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai na Vanguard.

Dangane da zaben gwamnan Anambra, “A bisa ga wannan furci, Ɓangaren Dokubo Asari ya tabbatar da cewa zabuka a jihar Anambra da sauran wurare a yankin Biafra dole ne a gudanar da su bisa ka’ida; cewa duk wani kauracewa zaben Anambra da sauran wurare ya kasance mara amfani, ba zai haifar da da mai ido ba kuma ba zai iya rushe tsarin zaben ba saboda dole ne wanda ya yi nasara ya fito daga karshe bisa la’akari da kakkausar murya da ya fito ya kada kuri’a ga wadanda suka zaba.

“Cewa ci gaba da yakin neman zaben kauracewa zabe da sauran munanan dabi’u wadanda ke da alaka da ci gaban fafutukar kafa kasar Biafra, daga baya an yi watsi da su, don haka dole ne a karaya nan take.

Advertisement