Al'umma

Direban tirela, yaron shi, tireloli 3 da tankar mai sun kone kurmus a Delta

An samu rahoton mutuwar mutane biyu direban tirela da yaron shi a kusa da mahadar Ohoror daura da hanyar gabas zuwa yamma a karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.

Kazalika an kona tireloli uku da wata tankar mai dauke da man fetur gaba daya.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 27 ga watan Janairu.

Advertisement

An samu labarin cewa wata tirela mai dauke da granite tana kokarin bi ta kan tankar man dake makare da danyen mai a lokacin da ta yi karo da tankar kuma ta kama da wuta.

Har zuwa lokacin mika wannan rahoton, gobarar na cigaba da tashi yayin da jami’an kashe gobara ke fafatawa don kashe wutar da ta tashi.

Advertisement