Tsaro

Denmark ta janye sojojinta daga Mali

Sojojin kasar Faransa a Mali

Kasar Denmark ta ce za ta fara janye dakarunta daga Mali bayan da gwamnatin rikon kwaryar kasar a wannan mako ta dage kan janyewar kasar cikin gaggawa, lamarin da ke zama wani katabus ga Faransa yayin da ayyukan tsaron da take gudanarwa a yankin Sahel suka fara barkewa.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun saka tsakanin kasar Mali da kawayenta na kasa da kasa da suka hada da hukumomin yankin da kuma kungiyar tarayyar turai da suka sanyawa Mali takunkumi bayan da gwamnatin sojan kasar ta gaza shirya zabe bayan juyin mulki guda biyu.

An kuma kara takun saka dangane da zargin cewa mahukuntan rikon kwarya sun tura wasu ‘yan kwangilar soji masu zaman kansu daga kungiyar Wagner da ke samun goyon bayan Rasha zuwa Mali, lamarin da wasu kasashen Tarayyar Turai suka ce bai dace da aikinsu ba.

Advertisement

Ministan harkokin wajen Denmark Jeppe yace, “Muna iya ganin cewa gwamnatin rikon kwarya ta Mali, ko kuma janar-janar din juyin mulkin, sun aike da wata sanarwa a daren jiya, inda suka sake nanata cewa ba a maraba da Denmark a Mali, kuma ba za mu amince da hakan ba.” Kofod ya fadawa manema labarai a ranar Alhamis. “Don haka mun yanke shawarar janye sojojinmu zuwa gida.”

Advertisement