Wasanni

Dembele dole ne ya sanya hannu kan sabon kwantiragi ko kuma ya bar Barca – Xavi

Kocin Barcelona Xavi ya yi gargadin cewa za a sayar da Ousmane Dembele daga kungiyar idan har dan wasan na Faransa ya kasa sanya hannu kan sabon kwantaragi.

Advertisement

Yarjejeniyar Dembele ta kare a karshen wannan shekarar kuma Xavi ya ce ana tattaunawa kan sabunta yarjejeniyar tsawon watanni biyar kuma kungiyar ba za ta iya jira ba.

“Ko dan wasan ya sabunta ko kuma mu nemi mafita ga dan wasan – babu wata yiwuwar,” in ji Xavi.

Advertisement

“Muna cikin wani yanayi mai sarkakiya kuma mun fito fili tare da Ousmane.

Yana son ya ci gaba da zama amma ba a amince ba don haka dole ne mu yanke shawara a kungiyance wato ko dai mu sabunta ko samun mafita.

“Abun kunya. Ya taka leda a kowane minti daya tun lokacin da na zama koci,” in ji Xavi, wanda ya karbi ragamar horar da Barcelona a watan Nuwamba.

Dembele ya koma Barcelona ne daga Borussia Dortmund a shekara ta 2017 a kan fam miliyan 96.8 na farko kuma mai yuwuwa ya tashi zuwa fam miliyan 135.5, duk da cewa dan wasan mai shekaru 24 a Nou Camp ya samu cikas sakamakon raunin da ya samu.

An danganta shi da kungiyoyi da dama da suka hada da Manchester United da Newcastle da kuma Liverpool.

Advertisement