Addini

Deborah Samuel: Kada a soki Musulmai akan kare Manzon Allah – Sheikh Ibrahim Maqari

Farfesa Ibrahim Maqari, Babban Limamin Masallacin kasa da ke Abuja a ranar Juma’a, ya tsoma baki kan cece-kuce da ake yi kan kisan Deborah Samuel, a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari (SSCOE), Sakkwato.

An yiwa Deborah dukan tsiya tare da kona ta har lahira saboda ɓatanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam a ranar Alhamis.

Deborah Samuel tana zaune tare da iyayen ta ne a unguwar Old Airport Road da ke cikin birnin Sakkwato, an zarge ta da cin mutuncin Manzon Allah (S.A.W) a wata gardama da abokan aikin ta a makaranta, wanda dag bisa kuma ka samu tabbacin cewa ta yi ɓatancin.

Da yake mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafin shi na Facebook, ya yi kakkausan kira akan musulmi su kare manzon Allah ba tare da suka ba.

“Ya kamata kowa ya sani cewa mu Musulmi muna da wasu sabbin layukan da ba dole ba ne a ketare su. Darajar Manzon Allah (SAW) ita ce a sahun gaba a cikin jajirtattun layukan mu. Idan har ba a magance koke-koken mu yadda ya kamata ba, to bai kamata a rika sukar mu ba saboda mun magance matsalolin da kan mu ba,” malamin ya lura.

Back to top button