Laifuku

Daruruwan mutane sun yi zanga-zangar nuna adawa da karuwar laifuka a Afirka ta Kudu

Daruruwan yan kasar Afirka ta Kudu ne suka gudanar da zanga-zanga ranar Laraba don nuna adawa da karuwar laifuka a Diepsloot da ke kusa da birnin Johannesburg, inda suka zargi yan sanda da gaza shawo kan laifukan da suke zargi kan bakin haure.

Mazauna yankin sun tare tituna da tarkace tare da kona tayoyi a yayin da suka yi tattaki zuwa ofishin yan sanda na yankin domin jin bukatun su.

“Mun gaji da yan kasashen waje ba bisa ka’ida ba da ke zaune a cikin al’ummomin mu. Su ne ke da alhakin yawancin laifuffuka a nan saboda ba za a iya gano sawun yatsun su ba,” wani mai zanga-zangar da ya bayyana kan shi a matsayin James ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency.

Yace suna bukatar yan sanda su gudanar da wani samame a yankin tare da duba halin shige da ficen duk wani dan kasar waje da ke wurin.

Masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa an kashe kusan mutane bakwai a karshen mako a garin amma yan sanda ba su yi kama kowa ba.

A wani lokaci, yan sanda sun harba gurneti da harsasan roba don tarwatsa masu zanga-zangar.

Back to top button