Kasuwanci

Dangote zai fara sarrafa danyen mai a watan Satumba

Sabuwar matatar mai ta Dangote za ta fara sarrafa danyen mai a kashi na uku na wannan shekara Q3.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da aka yi a wurin aikin da ke Legas a karshen mako.

A cewar Bloomberg, Dangote ya ce aikin injina a matatar ya kammala kuma “da fatan kafin karshen kashi na uku ya kamata mu kasance a kasuwa.”

Advertisement

Ya kara da cewa, kamfanin zai fara aiki da sarrafa ganga 540,000 a rana.

Dangote yace. “Cikakken samarwa na iya farawa watakila, a karshen shekara ko farkon 2023,” in ji shi.

Matatar man Dangote tana Legas akan kudi dala biliyan 19.

Matatar ta na girka ganga 650,000 a kowace rana kuma ana kyautata zaton fitar da matatar zai fi karfin biyan bukatun man Najeriya da kuma mayar da kasar da ta fi kowacce fitar da danyen danyen mai zuwa kasashen waje.

Advertisement