Kasuwanci

Dangote ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta hana fitar da Masara zuwa kasashen ketare

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Aliko Dangote ya shawarci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta dakatar da fitar da masara zuwa wasu kasashe na wani dan lokaci.

Attajirin dan kasuwar da ya kafa rukunin Dangote yayi wannan kiran ne saboda fargabar karancin masara da alkama a duniya.

Ya bayyana haka ne a taron masu sarrafa abinci na Najeriya karo na hudu.

Advertisement

Rasha da Ukraine tare sun ɗauki kusan kashi 30 cikin 100 na alkama da ake sayarwa a duniya.

Yawancin alkama ana kwaso su daga tashar jiragen ruwa na Bahar Black zuwa Afirka da Gabas ta Tsakiya.

Dangote yace karancin taki zai shafi noman hatsi kamar masara da alkama a duniya.

Ukraine da Rasha suna da kashi 13 cikin 100 da kashi biyu cikin 100 na masarar da ake fitarwa zuwa kasashen waje.

Kasashen kuma suna da alhakin hada kashi 56 na potassium da phosphate a duniya.

Dangote yace, “Za a samu karancin alkama da masara da kayayyaki masu yawa domin kamar yadda muke magana a yanzu Rasha da Ukraine suna yin kusan kashi 30 na urea a duniya da kashi 26 na sinadarin potash a duniya – da kuma phosphate din akwai daya na mafi girma a duniya.

“Za a samu karancin abinci gaba daya, ba za mu iya samun takin zamani a gaba ba, ba za mu ga illar ba a yanzu, amma nan da watanni biyu, uku masu zuwa.

Amurka ba za ta iya yin adadin ton ɗin da suka yi a bara ba saboda wannan.

“A yanzu za ka fara ganin mutane suna fitar da masara zuwa kasashen waje don samun kudin waje, wanda a ganina ya kamata mu daina, don kada mu yi karanci, kuma mu tabbatar mun kara noman don kada mu yi karanci ya shafi samar da abinci ne, kuma yana da matukar muhimmanci.”

Advertisement