Wasanni

Dan Kwallon Najeriya Ya Fadi Ya Mutu A Kasar Sifen

Dan kwallon Najeriya ya fadi, ya mutu a Spain.

Dan wasan kwallon kafar Najeriya, Hadi Ado Bala ya fadi ya mutu a wasan gida tsakanin kungiyarsa CD Madridejo FC da SP Cabanillas dake kasar Spain Terceira Division.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi.

Hukumar kwallon kafa ta Castilla-La Mancha a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce dan wasan na Najeriya ya fadi ba tare da wani dalili ba a minti na 39 na wasan.

Jami’an lafiya a filin wasa na Municipal Toledo an ce nan take suka kai masa dauki, amma kokarin farfado da shi ya ci tura domin daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

Haihuwar dan wasan Kafanchan mai shekaru 21, Hadi, ya fara wasan kwallon kafa ne da kungiyar Arewa United da wasu kungiyoyi da dama kamar Shareef Academy, Golden Balley, Zaria Bees da Salama FC duk a garin Kafanchan, kafin daga bisani ya koma jihohin Filato da Jigawa.