Damfarar Miliyan N40: Mama Boko Haram, Wasu Mutane Biyu Zasu Yi Shekara 10 Gidan Yari
An yankewa Aisha Alkali Wakil, wadda aka fi sani da Mama Boko Haram da wasu mutane biyu, Tahiru Saidu Daura da kuma Yarima Lawal Soyade an yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa samun su da laifin damfara ta Naira miliyan N40.
Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ce a ranar Litinin mai shari’a Umaru Fadawu na babbar kotun jihar Borno dake Maiduguri, ya yanke wa mutanen uku, Wakil, Daura, da Soyade hukuncin bayan da hukumar ta gurfanar da su a gaban kuliya bisa zarge-zarge biyu da suka hada da hada baki da kuma samun su ta hanyar karya wajen karbar Naira miliyan arba’in.
Kakakin EFCC ya bayyana a cikin sanarwar cewa Wakil, Daura, da Shoyade, babban jami’in gudanarwa, Manajan shirye-shirye, da kuma daraktan hukumar ta Complete Care and Aid Foundation, wata kungiya mai zaman kanta, da Saidu Mukhtar, a yanzu haka ya gudu, don zamba, su karbi Naira miliyan 40 daga Bashir Abubakar, Shugaban Kamfanin Duty-Free Shop Ltd, a bisa zargin aiwatar da aikin kwangilar da aka ce su samar da na’urorin X-ray guda biyar masu amfani da hasken rana.
A cewar Oyewale, laifin ya sabawa sashe na 1 (b) na dokar damfara da sauran laifukan da suka shafi zamba, na 2006, kuma hukuncin da aka yanke a karkashin sashe na 1 (3) na wannan dokar ne.
Wadanda ake tuhumar sun amsa “ba su da laifi” lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen.
Lauyan masu kara, A.I. Arogha, ya gabatar da shaidu hudu tare da gabatar da shaidu 17 a gaban kotun.
A dalilin haka mai shari’a Fadawu ya yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa laifin hada baki. Kotun ta kuma yanke wa Bashir Muhammad hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa laifin karbar kudu ta hanyar karya, ya kuma umurce su da su biya tare da biyan Naira miliyan N40 ga Bashir Muhammad.
Alkalin ya bada umarnin a gudanar da wa’adin gidan yari a lokaci guda.
Oyewale ya rubuta a cikin sanarwar cewa: “Tafiyar wadanda aka yankewa hukuncin zuwa gidan gyaran hali ya fara ne a lokacin da mai shigar da kara ya yi zargin cewa sun damfare shi ta hanyar wata kwangilar samar da na’urorin x-ray guda biyar 1900 da makamashin hasken rana ga wata kungiya mai zaman kanta, Complete Care and Aid Foundation, wanda kudinsu ya kai miliyan N40. Saboda ba su bada injunan ba ko kuma ba su mayar da kuɗin kwangilar ga mai ƙara ba.”