Tsaro

Damfara: An ba ƴan sanda wa’adin sati 2 su kammala bincike kan Abba Kyari

Hukumar kula da yan sandan Najeriya ta bayar da wa’adin makonni biyu ga rundunar yan sandan Najeriya da ta kammala bincike kan lamarin da ya shafi mataimakin kwamishinan yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari.

Wannan matakin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban, manema labarai da hulda da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar ranar Juma’a.

Hukumar ta kuma umurci yan sanda da su tabbatar da gudanar da binciken ta wani kwamiti na daban.

Advertisement

Umurnin dai ya biyo bayan babban taron hukumar ne karo na 14 a Abuja, wanda babban sufeton yan sanda kuma shugaban hukumar Musiliu Smith mai ritaya ya jagoranta.

Ku tuna cewa an dakatar da Mista Kyari ne a ranar 1 ga Agusta, 2021, biyo bayan shawarwarin da Sufeto Janar na yan sanda, Usma Baba ya bayar kan zargin alakar shi da dan damfara, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Dakatarwar ta biyo bayan rahoton da hukumar bincike ta tarayya ta Amurka ta fitar wanda ta tuhumi Kyari da laifin zamba da ya shafi fitaccen jarumin Instagram, Hushpuppi.

Kyari, har zuwa lokacin da hukumar ta dakatar da shi, shi ne jami’in da ke kula da tawagar da ke ba da amsa ga hukumar leken asiri ta yan sanda ta Sufeto-Janar.

Advertisement