Al'umma

Dalilai (5) da suka sa wasu ƴan Afrika ke goyon bayan Rasha a yaƙin ta Ukraine

Shugaba Putin a ƙasar Tanzania 1973

Ba sabon labari ne ga akasarin mutane ba cewa har yanzu qna cigaba da gwabza yaƙi tsakanin ƙasar Rasha da Ukraine.

Advertisement

Kawo yanzu an ƙiyasta cewa an asarar rayuka da dama a yaƙin ciki har fareren hula a kasar Ukraine bayan mamayewar da Rasha ta yiwa ƙasar a yan kwanaki baya.

Ko yau Litinin kamfanin dillancin labarai na AFP, ya wallafa a shafin yanar gizon shi cewa wani hari da Rasha ta kai a tsohon babban birnin kasar Ukraine Karkiev yayi sanadiyar mutuwar mutane 11, duk da tattaunawar zaman lafiyar ke gudana a yanzu haka.

Advertisement

Kasashen duniya da dama sunyi Allah-wadai mamayar Rasha, amma kuma har yanzu akwai wasu yan Afrika dake goyon bayan Rasha a wannan yaƙi bisa wadannan dalilai da zamu kawo a ƙasa;

1. A shekarar 1973 Vladamir Putin ya bar Rasha na tsawan shekaru huɗu ya tare a ƙasar Tanzaniya domin ya taimaki ƙasar wajen fafutukar korar Turawa ƴan’ mamaya da wawushe arziƙin Africa marasa ƙarfi, shekaru kaɗan bayan haka ya zama Shugaban Ƙasar Rasha.

2. Rasha ta taimaki ɗan gwagwarmayar neman ƴanci Patrick Lumumba na Angola kuma tayi yaƙi da shi wajen ƙulabalantar Africa ta kudu wacce a wancan lokaci take samun goyon bayan Amerika da Ingila da Faransa.

3. Rasha ta nuna goyon baya ɗari bisa ɗari ga Egypt a sanannen yaƙin nan da aka tabka wanda akaiwa laƙabi da ” Sinai war” (yaƙin Sinai).

4. Rasha ta taimaka sosan gaske wajen ƴan’tar da Mali daga hannun ƴan’ mulkin mallaka na Faransa, kuma ɗaruruwan sojojin ta aka kashe wajen fatattakar Faransawa daga Mali.

5. Rasha ta taimaki ƙasashen Africa da yawa ta hanyoyi daban – daban wajen taimaka musu domin gina ƙarfin soji da tattalin arziƙi da saida makamai domin yaƙar ƴan ta’adda, abun da Turai taƙi yiwa Africa saboda mafi yawan ta’addancin da yake faruwa a Afrika sune suka ƙirƙireshi. In kuma basu suka ƙirƙireshi ba to sune suke cin gajiyar faruwar shi.

Advertisement