Siyasa

Dalilai 2 da Tambuwal ka iya kayar da Mohammed ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP

A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Bala Mohammed a matsayin shugaban kasa a 2023.

Advertisement

Wike ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Gwamna Mohammed a jihar Bauchi. Gwamnan Ribas ya cigaba da bayyana cewa jam’iyyarsu ta Peoples Democratic Party, PDP, za ta fi samun damar lashe zaben shugaban kasa a 2023 idan Mohammed ya samu tikitin takara.

Da wannan, a bayyane yake cewa Wike ya yanke shawarar marawa Mohammed baya a maimakon tsohon abokinsa kuma amininsa na siyasa, Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato wanda shi ma yake sha’awar tsayawa takarar Shugaban kasa idan ya samu tikitin jam’iyyar.

Advertisement

1. Tambuwal za a iya cewa ya fi tasiri a Arewa: Tambuwal dai shine kakakin majalisar wakilai ta tarayya wanda ba a tsige shi ba duk da adawar da aka yi masa a lokacin. Takwarorinsa sun bashi goyon bayan ya cigaba da zama Shugaban Majalisar wanda hakan ya taimaka masa wajen kammala wa’adinsa cikin nasara.

Tambuwal ya kuma kalubalanci ubangidansa na siyasa ya sake lashe wa’adi na biyu a 2019 a karkashin PDP bayan ya fice daga jam’iyyarsa ta All Progressives Congress, APC. Hakan na nufin Tambuwal ya lashe kujerar Gwamna a karkashin jam’iyyar APC da PDP wanda hakan ya nuna cewa yana da farin jini na yin nasara a karkashin kowace jam’iyya.

Sannan kuma Tambuwal ya fi kowa sanin yan Najeriya musamman a Arewa kuma ya fi Mohammed tasiri a harkar siyasa fiye da Mohammed wanda ya zama Gwamna na farko.

Wannan al’amari zai iya taimaka masa wajen samun nasara akan Mohammed da sauran masu fafutukar neman tikitin takarar Shugabancin PDP.

2. Shiyyar Arewa na iya taimakawa Tambuwal: Tambuwal ya fito ne daga shiyyar Arewa maso Yamma mafi yawan jama’a kuma mai tasiri ba kamar Mohammed wanda ya fito daga Arewa maso Gabas ba.

Arewa maso yamma tana da jihohi bakwai (mafi girma a Najeriya) sabanin Arewa maso Gabas mai jihohi shida.

Dangane da karfin kada kuri’a jihohin Arewa maso Yamma sun fi sauran shiyyoyin Najeriya yawan kuri’u inda Kano ce ke kan gaba. Wannan yanki na iya fifita Tambuwal akan Mohammed.

Advertisement