Tsaro

Da Najeriya ta zama tarihi inda Buhari bai zama shugaban ƙasa ba – Gwamna Ayade

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya danganta cigaba da wanzuwar Najeriya da hawan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, yana mai cewa da yanzu kasar ta zama tarihi idan ba shine ba.

Ayade wanda ya yi magana a wani shirin gidan Talabijin na Channels, Sunrise Daily a ranar Laraba, yace kokarin da Buhari yayi wajen magance dimbin matsalolin da kasar nan ta fuskanta daga gwamnatocin da suka shude, shine ya sa kasar ta kasance tare har ya zuwa yau.

Ayade ya yabawa kokarin Buhari na magance matsalar rashin tsaro a kasar, inda ya jaddada cewa idan ba shugaban kasa yasa baki ta hanyar amfani da kwarewarsa ta soja wajen magance matsalar, da yan ta’adda da masu tayar da kayar baya sun gurgunta kasar nan kafin yanzu.

Advertisement

A cewar Ayade, “akwai wata makarkashiya da kasashen duniya suka kulla wa kasar nan, musamman yankunan Arewa” kuma da kasar ta ruguje da Buhari bai sa baki ba.

“Watakila, da ba gwamnatin Buhari da tarihin soja ba, da kasar ta ruguje a wannan matakin,” in ji Gwamnan.

“Mutane ba su san da hakan ba saboda idan kun sami damar gujewa haɗari, babu wanda zai iya ganin sa saboda an kauce masa. Ina ganin lamarin zai iya yin muni,” in ji shi.

“Tsaro yazo na farko kuma abin da Shugaba Buhari yayi a lokacin da ya hau karagar mulki shine na dakile hare-haren Boko Haram wanda ke da matukar muhimmanci don hana tada zaune tsaye a kasar.

“Da kasar nan ta ruguje idan ba don Buhari na soja ba kuma lamarin zai iya yin muni.

“Rikicin da muka tsinci kanmu a ciki da yafi rikicin ISIS a Gabas ta Tsakiya, don haka mu yan Najeriya mu yiwa Shugaba Muhammadu Buhari godiya,” inji shi.

Advertisement