Siyasa

Da Ɗumi-Ɗumi: APC ta dage babban taron ta na kasa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta dage babban taron ta da aka shirya gudanarwa da a farko ranar 26 ga Fabrairun nan na 2022.

An dai yi ta cece-kuce a kan cewa jam’iyya mai mulki za ta iya dage taron saboda matsalolin da ba’a warware ba kamar na shiyya-shiyya da kuma tashe-tashen hankula a wasu jihohin da take mulki.

An mika shawarar dage taron zuwa ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a wata wasika mai dauke da kwanan watan Fabrairu 21, 2022.

Advertisement

Sanarwar na dauke da sa hannun shugaba da Sakataren Kwamitin Tsare-tsare na Jam’iyyar APC na rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni, da kuma Sanata John James Akpanudoedehe.

Advertisement