Tsaro

Da Ɗumi-Ɗumi: An cafke masu satar mutane 3 ɗauke da bindigogi a kasuwar ‘Mamman Suku’

Rahotannin dake shigo muna a yanzu sun bayyana cewa an samu nasarar cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a wata kasuwar mako-mako dake ci ranar juma’a a garin Mamman Suka dake a karamar hukumar mulki ta Gwadabawa a jihar Sakkwato.

Wani mai cin kasuwar a kowace juma’a wanda aka (sakaye sunan shi) ya bayyana muna ta wayar tarho cewa kafin shiga sallar juma’a a yau dai-dai lokacin da kasuwar ke ci, an cafke wasu mutane 3 ɗauke da bindigogi.

Amma kamu dan kasuwar bai bayyana cewa an samu wani yamutsi ko tashin hankali ba kamar yadda wasu mutane ke yadawa.

Advertisement

“Abinda ya faru shine an kama wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane cikin kasuwar ta Mamman Suka dauke da bindigogi kimanin su 3, kuma in Allah yaso da mun gama sallah zamu bar kasuwar”. Inji shi.

Advertisement