Al'umma

“Da Ƙyar Na Tsira Bayan Ƴan Bindiga 3 Sun Nuna Bindigogin Su A Kaina – Inji Wani Da Ya Sha Da Ƙyaur

Wani da ya tsira da ransa bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane hudu a kauyen Barawa da ke jihar Katsina ya bayyana yanda ya sha da ƙyar bayan ƴan bindiga 3 sun nuna bindigogin su akan shi. Shi ma wani mutum da aka kashe kakarsa yayin harin shi ma yayi magana yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV.

Ayyukan ‘yan ta’adda da makami da kungiyoyin ‘yan bindiga wani batu ne dake damun ‘yan Najeriya da dama. Masu laifin sun yi kaurin suna wajen kashe-kashe da garkuwa da mutane da kwanton bauna a yankin Arewacin kasar nan.

Da yake bada labarin abin da ya faru, wanda ya tsira ya ce, da kyar na tsira ba’a kashe shi ba saboda 3 daga cikin ‘yan bindigar sun nuna mass bindigogi. Yace ya sami raunuka a cikin lamarin. Ƴan bindigar sun dage cewa ina da kudi a hannuna, amma na musanta. ‘Yan bindigar sun ce suna da niyyar kara cutar da al’umma.

Wani dan daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ya ce, “A gaskiya, jami’an tsaro sun yi iya bakin kokarinsu, amma sai sun dawo da dabarun yaki da ‘yan bindiga da makami. Kakata ita ce tsohuwa wadda aka kashe.”

Back to top button