Tsaro

China ta ce ƴan ƙasar ta fiye da 3,000 suka bar Ukraine

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai cewa, sama da yan kasar Sin 3,000 ne aka kwashe daga kasar Ukraine zuwa kasashen da ke makwabtaka da su cikin koshin lafiya.

Ba kamar ƙasashe da yawa ba, China ba ta gayawa kusan yan ƙasar ta 6,000 a Ukraine da su bar ƙasar ba a kwanakin da suka kai ga mamayewar Moscow.  Madadin haka, Beijing ta ba da sanarwar shirin ficewa jim kadan bayan an fara kai harin.

Advertisement
Advertisement