Siyasa

China da Netherlands zasu inganta dangantakar su da hadin gwiwa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana a jiya Juma’a a birnin Beijing cewa, ya kamata kasashen Sin da Netherlands su yi amfani da damar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya da kulla huldar diplomasiyya da juna.

Wang ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan kuma ministan harkokin wajen kasar Wopke Hoekstra, inda ya kuma taya Hoekstra murnar samun sabon mukamin.

Da yake kiran kasar Netherlands muhimmiyar abokiyar huldar Sin dake nahiyar Turai, Wang ya ce, kasar Sin na mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar.

Advertisement

Ya kara da cewa, tare da hadin gwiwar shugabannin kasashen biyu sun bayyana matsayar kulla huldar abokantaka ta gaskiya da adalci, don samun cikakken hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, wanda ke nuna cikakken yanayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma burin ci gaba a nan gaba.

Advertisement