Siyasa

Chadi: Gwamnatin Soji da kungiyoyin ƴan adawa na gudanar da tattaunawar sulhu a Qatar

Karamin ministan harkokin wajen Qatar Sultan bin Saad Al-Muraikhi (Hannun Dama) ya gana da firaministan kasar Chadi Albert Pahimi Padacke a farkon tattaunawar sulhun kasar Chadi.

Gwamnatin mulkin sojan Chadi da dimbin ƴan kungiyoyin adawa sun fara tattaunawar zaman lafiya a ƙasar Qatar a matsayin matakin farko na kawo karshen tawaye da gudanar da zabe a kasar.

An gayyaci wasu kungiyoyin yan tawaye da yan adawa 44 masu dauke da makamai zuwa taron Doha – ko da yake wasu basu halarci bude taron a ranar Lahadi ba, wanda tuni aka jinkirta daga ranar 27 ga Fabrairu.

Firaministan kasar Chadi Albert Pahimi Padacke da shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat sun shaidawa taron cewa, dole ne bangarorin biyu su yi sassauci don samun nasara a tattaunawar. Amma tsarin yana yin haɗari da tsayi da rikitarwa.

Advertisement
Advertisement