Kasuwanci

CBN Ya Rage Kuɗin Da Za’a Iya Cira Daga Asusun Banki Zuwa ₦20,000 A Kullum Da ₦100,000 A Sati

A ranar Talata ne babban bankin Najeriya CBN ya fitar da wani sabon umarni ga dukkan bankunan da ke nuni da cewa kar a fitar da tsabar kudi ta hanyar bankuna da ya wuce ₦100,000 na mutum daya da kuma ₦500,000 ga kamfanoni a sati.

An rubuta wannan ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Haruna. B. Mustapha daraktan kula da harkokin bankuna yayin da ya bayyana cewa duk daidaikun mutane za su iya cire kudi naira ₦100,000 ne kawai a duk mako daga ma’ajiyar su, wurin sayar da kayayyaki (POS) da na’urar ATM da kamfanoni kawai za su samun ₦500,000 duk sati.

Haka kuma bankuna an bukaci su sakawa mashin din su na Automated Teller Machine (ATM) takardun kudi na ₦200 da sauran kananan kudade kawai.

Advertisement

Babban bankin ya kuma bayyana a cikin takardar cewa, adadin kudin da mutum zai fitar a kullum bai kamata ya wuce ₦20,000 a kullum ta hanyar sayar da kayayyaki (POS) da kuma Automated Teller Machine (ATM).

CBN ya kuma shawarci duk abokan huldar bankin da su yi amfani da apps na banki daban-daban, USSD code, eNaira wajen hada-hadar kasuwanci.

Advertisement