Kasuwanci

CBN Ya Fara Raba Sabbin Kuɗin Naira Da Aka Sake Fasalin Su Ga Bankuna

Gwamnan babban bankin kasa (CBN) ya ce ya fara rabon kudaden naira da aka yi wa kwaskwarima ga bankunan ajiya na kudi (DMBs) domin cigaba da yawo ga jama’a.

Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya tabbatar da hakan a gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari na Daura a jiya.

Emefiele ya kai wa Buhari ziyara ne biyo bayan kin amincewar da Majalisar Tarayya ta yi kan shirin CBN na kakaba takunkumi kan fitar da kudade daga ranar 9 ga watan Janairu. A karkashin sabon tsarin CBN na cire kudaden da kungiyoyi da daidaikun mutane ke cirewa a kan teburi a duk mako shine N100,000 da N500,000.

Advertisement

A cewar CBN, ba zai yi tsauri da manufar ba saboda zai rika bitar ta lokaci zuwa lokaci. Da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar, Emefiele yace Buhari ya yi farin ciki da wannan manufa kuma ya bukace shi da ya cigaba, yana mai ba shi tabbacin “kada ya ji tsoro; babu bukatar damuwa da kowa”.

Yace: “Na ziyarci Daura ne don ganin Shugaban kasa da kuma gaishe shi a wani bangare na bayanin da na saba yi. “Tattaunawar ta wuce lokaci kuma na yi tunanin ya kamata a yi masa bayanin abubuwan da ke faruwa a babban bankin kasa, abubuwan da ke faruwa a tattalin arziki. “Akwai abubuwa da yawa da ke faruwa, batutuwan da suka shafi kudin.

A jiya ne dai sabbin kudaden suka isa bankunan, kuma muna sa ran bankunan za su fara rarraba kudaden ga jama’a da kwastomomi; da kuma tabbatar wa shugaban kasa cewa al’amura suna tafiya yadda ya kamata game da kudin da kuma batun da ya shafi tsarin rashin kudi da muka bullo da shi kwanan nan.”

Advertisement