Kasuwanci

Canjin Dala: An canja Naira ₦416 akan $1 a kasuwan gwamnati

A ranar Alhamis, farashin Naira da dala ya tsaya cak a bangaren masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki (I&E) na kasuwar canjin kudin kasashen waje.

Bayanan FMDQ sun nuna cewa Naira ta rufe kasuwancin ranar Alhamis a kan ₦416.33/$1 daidai da farashin da ta rufe a ranar Laraba.

Kwanciyar hankali na kudin Najeriya ya faru ne yayin da farashin FX ya ragu da kashi 16.4 cikin dari ko kuma dala miliyan $20.47.

Advertisement

Masu hada-hadar a ranar Alhamis sun yi cinikin dala miliyan ₦104.10 idan aka kwatanta da dala miliyan $124.57 da aka ruwaito kwana daya da ta gabata.

Sai dai kuma, darajar kudin cikin gida ta cigaba da faduwa idan aka kwatanta da na Amurka a bangaren bankunan kasuwar, inda a jiya aka yi asarar kobo 15 a kan ₦415.45/$1 idan aka kwatanta da na ranar da ta gabata ta ₦415.30/$1.

Amma ta kara daraja da ₦1.04 a kan Fam Sterling a ranar Alhamis inda aka sayar da shi a kan ₦565.18/£1 sabanin farashin ranar Laraba na ₦566.22/£1 da Yuro, Naira ta yi asarar kobo 17 inda aka sayar da ita kan ₦471. 16/€1 idan aka kwatanta da ₦470.99/€1 na zaman karshe.

A kasuwar bayan fage dai Naira ta dawo da kadan zuwa ₦578/$1 a kan dala daya bayan da ta ci ₦580/$1 a kwana daya.

Advertisement