Tsaro

Buhari ya sake tabbatarwa yan Najeriya zai murkushe yan ta’adda da yan bindiga

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake jaddadawa yan Najeriya kudirin gwamnatinsa na kawarsuwa tare da murkushe yan ta’adda da yan fashi da sauran masu aikata miyagun ayyuka da suke yi a sassan kasar nan kafin cikar wa’adin mulkinsa.

Buhari, wanda ya bayar da wannan tabbacin a ranar Juma’a a wajen wani liyafa da Gwamna Nasir El-Rufai ya shirya don karrama shi a karshen ziyarar aiki ta kwanaki biyu da shugaban kasa ya kai jihar Kaduna, yace munanan ayyukan yan bindiga a jihar da sauran sassan kasar nan ba da jimawa ba za su zama tarihi.

‘Ina so in tabbatar wa al’umma da gwamnatin jihar Kaduna da ma yan Nijeriya baki daya cewa gwamnatin tarayya na yin iyakacin kokarinta wajen ganin ta dakile tare da murkushe yan ta’addan da ke yi wa ‘yan kasa barazana da dukiyoyinsu a sassan kasar nan.

Advertisement

“A madadin gwamnatin tarayya, ina yabawa kokarin gwamnatin jihar Kaduna na amsa bukatun ci gaba da kuma daukar matakin gaggawa kan kalubalen tsaro a jihar.

Advertisement