Siyasa

Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe da aka yiwa kwaskwarima

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar gyaran zabe ta 2021 ta zama doka.

An yi bikin rattaba hannu kan dokar ne a cikin zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja da misalin karfe 12:30 na safiyar yau Juma’a.

Daga cikin wadanda suka halarci taron, yayin da shugaban kasar ke amincewa da kudirin ya hada da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Mahmood Yakubu; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da sauran su.

Advertisement

Rattaba hannun dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gamayyar kungiyoyin farar hula suka gudanar da zanga-zangar neman tilastawa shugaban kasar amincewa da takardar da aka yi wa kwaskwarima.

Advertisement