Kasuwanci

Buhari ya dawo amfani da Twitter bayan ɗage wa kamfanin haramci aiki a Najeriya

A ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa a shafin shi na Twitter a karon farko tun bayan da Najeriya ta dage haramcin shiga shafin Twitter.

A watan Yunin 2020 ne gwamnatin Najeriya ta sanya dokar hana shiga shafin Twitter.

Haramcin ya biyo bayan shawarar da Twitter ya yanke na goge sakon Twitter da Buhari ya wallafa a shafin shi.

Sakon Twitter, wadanda yayi magana game da yakin basasar Najeriya, yayi yi barazanar magance wadanda ke haddasa rashin tsaro a cikin “harshen da suka fahimta”.

Back to top button