Tsaro

Buhari ya dage ziyarar da ya shirya zuwa Zamfara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage ziyarar da zai kai jihar Zamfara wacce da aka shirya gudanarwa a yau Alhamis.

Gwamna Bello Mattawale wanda ya bayyana haka ya bayyana rashin kyawun yanayi a matsayin dalilin soke ziyarar shugaban kasar zuwa jihar.

Zamfara ta kasance cibiyar yan ta’adda da ta’addancin ƴan bindiga a cikin yan shekarun nan. Gwamnan da kansa ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wasu miyagu suka kaiwa ayarin motocinsa hari fiye da sau daya.

Advertisement

Matawalle ya sanar a ranar Alhamis din da ta gabata cewa, shugaban kasar da aka shirya ya tashi daga Sokoto a cikin jirgi mai saukar ungulu, ya dage ziyarar ne saboda rashin kyan gani.

“Shugaban kasa ya yi magana da ni kuma ya bukace ni da in isar da uzurinsa ga mutanen jihar. Shugaban ya ce a mako mai zuwa zai sake dage ziyarar zuwa jihar kuma za a sanar da mu ranar da aka kayyade idan lokaci ya yi.

Advertisement