Al'umma

Buhari Ya Aika Saƙon Allah Ya Bada Lafiya Zuwa Ga Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din da ta gabata ya yiwa Sheikh Mohammed Dahiru Bauchi fatan samun sauki daga rashin lafiya.

Shugaban a sakon da ya aikewa jagoran kungiyar Tijjaniyya ta Darikar Tijjaniyya, wanda Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Ibrahim Ali Pantami ya mika a madadin shi, yace yana yiwa Sheikh fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Shugaba Buhari yayi addu’ar Allah ya kara wa jagoran addinin Musulunci lafiya, domin manyan koyarwar shi ta cigaba da jagorantar al’umma da mabiyan shi a kokarin samar da al’umma mai adalci da jin kai, a cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar. A cewar Daily Trust.

Advertisement

Tunanina yana tare da shi. Ya kara da cewa, “Allah ya ba shi lafiya da samun sauki cikin gaggawa.

Pantami ya sanar da shugaban kasar cewa halin da Sheikh din yake ciki ya samu sauki sosai.

Jagoran addinin Musuluncin ya kuma bayyana godiyar shi ga shugaban kasar bisa yadda ya nuna damuwar shi da kuma fatan alheri, sannan ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da samun nasara wajen samar da zaman lafiya da ci gaba da gina kasa.

Advertisement