Tsaro

Buhari na kallon Kanu, Igboho a matsayin barazana, zai sake su bayan zaben 2023 – Giwa

Fitaccen malamin addinin nan na Najeriya Fasto Adewale Giwa, ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta saki jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu bayan zaben 2023.

Malamin Kiristan ya kuma bayyana cewa za a saki fuskar da aka sani na tayar da kayar baya ga kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, daga jamhuriyar Benin bayan zabe.

Fasto Giwa, wanda ya bayyana hakan a karshen mako, yace gwamnatin shugaba Buhari tana kallon masu tada zaune tsaye a matsayin barazana ga zaben 2023.

Advertisement

Ya kara da cewa, domin gudun kada a samu tarzomar da ke kara ta’azzara a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso yammacin kasar nan, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar cafke su ta kowace hanya tare da hana su shiga cikin jama’a har sai an kammala zabe.

Advertisement