Siyasa

Buhari Bazai Taba Goyon Bayan Tinubu ba Inji Sule Lamido

Buhari Bazai Taba Goyon Bayan Tinubu ba Inji Sule Lamido

Ayaune tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido yafito ya bayyana cewa yasan mutanen da Buhari yakeson su gajeshi, inda Daga baya ya bayyana cewa bazai taba Yadda Tinubu ya karbi mulki ba.

Alhaji Sule Lamido, Wanda babban Jagorane a Peoples Democratic Party wato (PDP), ya bayyana cewa yana tunanin za’a juyin mulki acikin zaben fidda gwani da APC zasuyi.

Wannan juyin mulki ne zai kai ga samar da tikitin shugaban kasa na shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, Inji Sule Lamido.

Lamido ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ya zama shugaban kasa ba saboda tunaninsa.

Kamar yadda Lamido yafada da bakinsa cewa:

“A yanzu haka, Tinubu na tsaka mai wuya daga wa? Yan uwansa a kungiyar Afenifere wadanda suka fito karara suka nuna basa son shi da kuma gwamnonin APC da suka suna basa son shi saboda sun ce yana da izza da iko. Ina nufin, shi dansu ne, me zai sa ba za su iya sanya shi ba? “Ku lura da maganganuna, Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ba. Na san tunanin mutumin. Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba. Na fada amma mutane basu yarda dani ba amma ku zuba ido ku gani. Abun gaba daya ba game da Tinubu bane ko ra’ayin wasu. Ba ma don Najeriya bane sai don wasu muradai na gashin kai. Babu yadda za a yi Buhari ya marawa Tinubu baya, saboda gaba daya abun zai karkata ga ra’ayin kai.

“Mu yi magana ta gaskiya, a yau Tinubu yana rawarsa ne shi kadai. Dubi abun da ya yi amma a yanzu suna ce masa a’a.

“Idan kudu ta shirya lashe zabe, dan takara daya da zai iya fafatawa da PDP don kudinsu shine Tinubu. Yana da nufi mai kyau. Yana da iyali na siyasa. A Najeriya a yau, koda APC bata bashi tikiti ba, zai lashe zabe saboda Najeriya na son komai baya ga Buhari. “Na fadi Buhari ba zai ba Tinubu ba, yana kokarin hada Amaechi da Lawan. “Ina hangen juyin mulki.”

Aika Da Wannan Labarin: