Siyasa

Buhari bai bayar da umarnin cire tallafin man fetur ba – Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, yace a ranar Talata shugaban kasa Muhammadu Buhari bai bayar da umarnin cire tallafin man fetur a kasar ba.

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta umurci dukkan majalisun jihohin kasar da su tara mambobinta domin gudanar da zanga-zangar kwana daya a fadin kasar a ranar 27 ga watan Janairu, kan shirin cire tallafin man fetur da kuma sanya harajin kashi 10 cikin 100 na kayan shaye-shaye da gwamnatin tarayya ta yi.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ta yi a watan Oktoban shekarar da ta gabata cewa gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin man fetur ne kawai na watanni shida na farkon shekarar 2022.

Advertisement

Lawan, wanda ya yi wa manema labarai jawabi bayan ganawar sirri da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja, yace majalisar ta damu da tashe-tashen hankula da zanga-zanga a fadin kasar.

Yace: “To, zai zama abin sha’awa ga yan Najeriya su ji abin da na zo don tattaunawa da Shugaban kasa da wasu abubuwa da dama.

Da yawa daga cikinmu sun damu matuka da tashe-tashen hankula da zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan, da yawan yan kasa sun damu matuka, al’ummar mazabarmu a fadin kasar nan sun damu matuka cewa gwamnatin tarayya za ta cire tallafin man fetur. Kuma a gare mu a matsayinmu na yan majalisu masu wakiltar al’ummar Nijeriya, wannan ya shafe mu.

Kuma mun gama hutun mu, da mun je gida mazabunmu da gundumominmu na majalisar dattawa. Kuma za mu ji bugun jini na mutanenmu. Kuma na ga ya dace in ziyarci shugaban kasa a matsayinsa na jagoran gwamnatinmu kuma jagoranmu a kasar, domin tattauna wannan batu da ya shafi yan Nijeriya, kuma ina mai farin cikin sanar da yan Nijeriya cewa, shugaban kasa bai taba gayawa kowa haka ba na maganar a cire tallafin man fetur.” Inji Lawan.

Advertisement