Tsaro

‘Boko Haram wasar yara ce idan aka bari ISWAP ta girma’ – Gwamna Zulum

Mai girma Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Alhamis, ya koka kan barazanar da kungiyar IS ta ke yi a yankin yammacin Afirka (ISWAP) da kuma kasar.

Zulum, wanda ya bayyana hakan a taron tattaunawa na mako-mako na tawagar shugaban kasa kan harkokin sadarwa a fadar gwamnati da ke Abuja, yace Boko Haram za ta zama wasan yara idan aka bar ISWAP ta yi girma a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ya kuma bukaci sojojin Najeriya da su sake yin dabara da kuma duba masu tayar da kayar baya domin amfanin yan kasa.

Advertisement

Gwamnan yace: “Yawancin ‘yan ta’addan ISWAP a wasu sassan jihar abin damuwa ne ga kowa da kowa, musamman a gabar tafkin Chadi da kuma kudancin jihar Borno.

Bari in bayyana a sarari, bai kamata mu bar ISWAP ta yi girma ba. ISWAP sun fi ƙwarewa, sun fi samun kuɗi kuma sun fi ilimi. Dole ne mu yi duk mai yiwuwa don kayar da ISWAP. Idan ba haka ba, abin da Boko Haram suka yi zai zama wasan yara. Wannan wani gargadi ne na farko da dole ne Sojojin Najeriya su sake tsara dabarun yaki da kungiyar ISWAP.

“ISWAP za ta zama barazana ga daukacin al’ummar kasar. Saboda kusancin da kungiyar take da yankin kudu da hamadar Sahara, suna zuwa daga Libya da sauran su don sake tsugunar da su a nan.

Advertisement