Tsaro

Boko Haram Sun Kai Hari Makarantar Horas Da Ƴan Sandan Najeriya, Sun Sace Masu Bada Horo

Nigeria Police

A ranar Alhamis din da ta gabata ne ‘yan kungiyar ta’adda ta Boko Haram suka kai farmaki makarantar horas da yan sanda dake karamar hukumar Limankara Gwoza a jihar Borno inda suka yi awon gaba da mutane da dama.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, masu garkuwan sun tafi da wasu ‘yan sandan da ba’a tantance adadinsu ba.

Makarantar horarwa tana kilomita ashirin da biyar daga garin Gwoza, mahaifar Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattawa akan sojoji. Gari ne mai iyaka tsakanin Borno da karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Advertisement

Rahotanni sun ce mayakan ‘yan tada kayar bayan sun kai hari makarantar horon ne a daren ranar Alhamis da manyan bindigogi inda suka rika harbin iska kafin su yi awon gaba da malaman yan sandan.

Harin dai na zuwa ne kwanaki bakwai bayan da ‘yan ta’addan suka yi yunkurin kutsawa cikin sansanin sojojin Najeriya da ke Gwoza inda wasu sojojin Najeriya suka yi nasarar fatattakar su.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji karkashin jagorancin Sanata Ali Ndume ya kai ziyarar aiki zuwa rundunar Operation Hadin Kai da ke yankin kwanaki biyu da suka gabata.

Advertisement