Tsaro
Boko Haram sun kai hari garin Chibok a Borno

Rahotanni sun ce mayakan Boko Haram sun kai hari kauyen Piyemi da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno a ranar Alhamis.
Wannan dai shine hari na biyu da aka kai wa al’ummar Chibok cikin kwanaki biyar.
Mayakan jihadin sun kashe mutane hudu a ranar 15 ga watan Janairu tare da yin garkuwa da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba yayin wani hari da suka kai kauyen Kautikari da ke yankin.
Mazauna garin sun shaida wa manema labarai cewa maharan sun kai farmaki kauyen ne da karfe 6:33 na yamma. sannan suka fara harbe-harbe ta bangarori daban-daban.
Sun kuma kona gine-gine tare da kwashe dabbobi da kayan abinci na al’umma.